Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Adamawa Ta Tabbatar Da Bullar Ciwon Cholera a Mubi

IDP Camp Cholera_2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa dake arewa maso gabashin najeriya ta tabbatar da bullar ciwon Cholera a Mubi inda wadanda suka kamu da cutar sun karu zuwa 434, 13 kuma suka rasu. Mai yada labarai na ma’aikatar Mr Abubakar Muhammed ya tabbatar da hakan a rahoton da ya fitar a Yola.

Haka nan shugaban asibitin Mubi General Hospital Dr Ezra Sakawa ya kara da cewa yawancin wadanda suka kamun sun samu sauki an sallame su.

Mubi dai ta samu bullar ciwon sati 2 da suka gabata inda ake ganin hakan nada nasaba da rashin kyan ruwan da suke dashi.

Kimanin kashi 90 na mutanen Mubi na siyan ruwa ne a gurin masu saida ruwa, inda su kuma suke debowa daga rijiyar burtsatsai da akayi don ban ruwan rani wanda ke zuwa daga kogin Yedzaram.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply