Ma’aikatan kiwon lafiya su 7 suna hannun yan sanda sakamakon karkatar da gidajen sauro dubu dubu 5 da dari 4 da 50 a jihar Gombe.

Ma’aikatan kiwon lafiya matakin farko su 7 kananan hukumomin Kwami da Billiri na jihar Gombe suna hannun yan sanda sakamakon karkatar da gidajen sauro dubu 5 da dari 4 da 50 da aka tanada domin rabawa yankuna.

Gidan radiyo Dandal kura ta rawaito cewa gwamnatin jihar tare da taimakon Global Fund, Catholic Relief Services da kuma shirin kawar da cutar maleriya ta kasa su suka tallafa da gidajen sauron.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Gombe Dr. Habu Dahiru ya bayyanawa manema labarai a wani taro a jihar Gombe cewa wadanda ake zargin an kama su ne a ranar 10 ga watan Satumba.

Yace an samar da gidan sauron ne domin rage matsalar cutar maleriya a jihar musamman ma a tsakanin mutane marasa karfi, yara da mata.

Ya kara dacewa an kama wadanda ake zargin ne ta hanyar ma’aikaci da yake da alhakin kula da yanayin kayakin domin tabbatar da cewa bai shiga hannun wadanda basu dace ba.

Sun tara gidajen sauron inda suka zba a cikin babbar mota a kasuwar Gombe da niyyar fita da shi.

Dahiru ya kara dacewa an karbo jerin gidajen sauro dari a Kwami sannan tara kuma a Billiri ya kara dacewa za’a raba su ga wadanda akayi domin su a kananan hukumomin 2.

Daga karshe ya yaba da kokarin jami’an yan sanda, hukumar tsaron farin kaya da kuma mambobin hukumar tsaron civil defence da kuma al’ummar gari wajen tabbtar da kama masu laifin.