Kwamitin Shugaban Kasa Kan Cutar Covid-19 Ta Bayyana Cewa Jihar Kogi Na Tsaka Mai Wuya

images (45)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin shugaban kasa mai kula da cutar covid-19 ta bayyana jihar kogi a matsayin wadda take cikin tsaka mai wuya a mtsayin wadda taki ta yarda da annobar ta covid-19, da kin bayyana sakamakon gwaji dakuma rashin samun gurin kebance masu kamuwa da cutar. Kwamitin ta kara da gargadin yan Najeriya dasu zama masu lura da kula yayin dasuke ziyartar jihar.

An gudanar da bincike kan cutar ta covid-19 a kasar, inda aka samu kananan hukumomi 22 masu fama da cutar tsakanin jihohi 13 dake kasar.

Manaja mai lura da hana kamuwar cutar ta covid-19 Dr Mukthar Muhammed ya bada takaiccecen bayani kan covid-19.

A bayanin Muhammed, yace kananan hukumomin guda 22 dake tsakanin jiha 13 a kasar, yawanci daga manyan biranen jihohin ne, wanda hakan ya kara fiyeda kaso 95 cikin sabbabin masu kamuwa da cutar a sati 6 dasuka wuce.

Ya bayyana jihohin da kananan hukumomin kamar haka; Nkanu West (Enugu), Babban Birnin Abuja da kewayen ta,Gwagwalada dake Abuja, Gombe (Gombe), Chikun (Kaduna), Kaduna North, Kaduna South, Nassarawa (Kano), Katsina (Katsina), Ilorin South (Kwara), Ilorin West, (Kwara), Eti-Osa (Lagos), Ikeja (Lagos), Kosofe (Lagos), Lagos Mainland, (Lagos), Keffi (Nasarawa), (Lafia) Nasarawa, Ibadan North (Oyo), Jos North (Plateau), Jos South (Plateau), Port-Harcourt (Rivers) and Wamako (Sokoto).

Yace, kwamitin ta shugaban kasa mai kula da cutar covid-19 tana aiki wajen kawo taimako ta hanyoyi da dama da kuma tabbatar da dokar da shugaban kasar ya rattabawa hannu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply