Kwamitin Karta Kwana Kan Yaki Da Cutar COVID-19 Na Jihar Kano Ta Gabatar Da Tsarin Bada Lafiya A Gida-Gida Duk A Cikin Kokarin Ta Na Dakile Bazuwar Annobar.

corona vaccine
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin karta kwana na yaki da cutar COVID-19 na jihar Kano ta gabatar da tsarin bada lafiya a gida-gida duk a cikin kokarin ta na dakile bazuwar annobar.

Hakan yana kunshe a cikin sanarwa da jami’in labarai na ma’aikatar lafiyan jihar a matakin fari, Maikudi Marafa ya fitar ranar asabar.

Sanarwar na kunshe da cewa, kwamishinan jihar Dr Aminu Tsanyawa ne ya kaddamar da shirin ranar asabar daya gabata wanda yace anyi hakan ne domin dakile bazuwar cutar karo na biyu, hade da cewa tuni an baiwa ma’aikatan lafiya horaswar, kuma an basu magunguna da Babura da nufin bada kulawa a wurare dake da wuyan shiga a yankin.

Haka zalika, Dr Tsanyawa ya bukaci ma’aikatan lafiyar dasu dukufa wajen sauke nauyin aiki da aka daura musu.
Sanarwar na kuma kunshe da cewa, shugaban kwamitin na jihar kuma babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar Kano, Dr Tijjani Hussain, yace shirin zaiyi amfani ne da samfurin yankin inda ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa irin gudumawa daya ke baiwa kwamitin yakar annobar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply