Kwamitin Kare Hakki Ta Duniya Ta Yi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Kara Kaimi Wajen Aikinsu Na Ceto Mutana.

world
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin kare hakki ta duniya ta kasar Switzerland a najeriya tace bata jin dadi a game da yadda ba’a daukan mataki da ya dace a game da kwato yan makarantar sakandari dake kankara a jihar katsina bayan shafe sati daya a hannun yan bidiga.

Yan bindigar da ake zargi da cewar yan ta’adda ne sun shigo makarantar ne a ranar juma’a da misalin karfe Goma sha daya na rana akan Babura.

A cikin wata sanarwar da shugaban kwamitin Ibrahim Ladan, ya bayar, yace ada chan baya yan bindigan sun kai hari zuwa garin kankarar tare da jikkata mazauna garin daga bisani jami’an tsaro suka korasu.

Kwamittin ta mika jajenta ga gwamnatin tarraya tare da gwamnatin jihar katsina da kuma iyaye da kuma malaman daliban da abun ya shafa.

Kwamitin ta yaba da kokarin da jami’an tsaro suke yi wajen yaki da yan ta’ada a cikin kasar amma tace bata ji dadi yadda ake kokarin mantawa da abunda ya faru a garin kankara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply