Kwamitin Gyare-Gyare Ta Gwamnatin Taraiya Sun Ziyarci Jihar Borno

images (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri 19 02 2021
Kwamitin gyare-gyare ta ziyarci Guzamala da Kukawa tareda alkawrin gina gidaje 320, makarantu, guraren samun ruwa 4, asibitoci, samar da wutar lantarki da kuma gina sabon fada na hakimin yankin na Mairi, cross Kawa da Baga.

Kwamitin daya samu zaman kwamishina na hukunci kuma babban alkali na jihar Barrister Kaka Shehu Lawan na aiki tukuru wajen samawa yan gudun hijiran dake sansanin Monguno da Maiduguri muhallai.

Idan za’a ayi tuna baya, gwamnan jihar borno farfesa babagana umara Zulum, ya kafa kwamitin a 31th na watan agusta a shekarar 2020.

Mambobin kwamitin sun samu rakiyar shugaban karamar hukumar Umar Kyari da wasu mambobin gwamnati, a yayin ziyarar zuwa Mairari dake karamar hukumar Guzamala hanyar Monguno.

Kwamitin ta kara zuwa cross Kauwa dake karamar hukumar Kukawa domin duba ayyukan dake kan gudana da duba yadda karfen sadawa na airtel dakuma yadda za’a maida mutanen cross kauwu.

A madadin gwamnan jihar borno farfesa Babagana Umara Zulum, shugaban kwamitin ya nuna yabawarsa ga dukkan matakan tsaron wajen kokarin su na taimakon gwamnatin ta hanyoyi daban-daban.

Shugaban karamar hukumar Guzamala da Kukawa, umar kyari da bukar aji sun yabawa gwamnan jihar wajen jajircewarsa dakuma sadaukarwa wajen gyaran garuruwan da yan ta’addan suka bata dakuma maida wadanda suka bar garuruwansu sakamakon ta’addanci.

Sun kara yabawa jami’an tsaro wajen sadaukarwar da sukayi don yaki dan ‘yan ta’addan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply