Kwamishinan Lafiya Na Jihar Borno Yace Har Yanzu Cutar Cizon Sauro Na Kisa A Najeria.

Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin jihar Borno karkashin gwamna Babagana Zulum farfesa Isa Marte, wanda kuma shine kwamishinan lafiya na jihar yace har yanzu cutar cizon sauro na daya daga cikin cutuka masu kisa a Najeria.

Ya bayyana hakan a bikin ranar cutar ta duniya wanda inda yace yana musun rahoton shekarar da ta gabata wanda ya nuna cewa Najeriya naci gaba rike da kashi 25 na mutanen duniya masu dauke da cutar dake kisa inda har yanzu ake da fiye da 80,000.

Farfesa Marte ya bayyana hakan a jiya ranar bikin a Maiduguri, inda yace ana gudanar da biikin ranar kowane 25 ga watan Aprilu don wayar da kan jama’a kan cutar da take lakume rayuwa fiye da biliyan 3 a fadin duniya.

A bikin na wan nan shekarar Marte yace abun yazo lokacin da ake fama da annobar Coronavirus wadda har yanzu ta addabi duniya.

Haka nan bikin na shekarar nan ya bada damar bayyana muhimman abubuwa kan cutar musamman lokacin da ake fama da rikici.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Borno ta shirya shirinta na shekaru 10 kan yaki da cutar a fadin jihar ta hanyar taimakon kudi daga Bankin duniya.