Kwamishinan al’amuran addini na jiha ya nemi jama’a da a tsananta addu’a cikin bukukuwan salla

Kwamishinan al’amuran addini na jihar Borno Hon. Alh Abatcha Umar Ngala ya taya al’umman musulmi murnar kammala azumin ramadan da kuma bikin karamin salla

Yayin gnawa da wakilin mu, Alhaji Umar Abatcha ya yabi malaman addini da irin jajircewar su wajen yiwa al’umma hidima kuma yayi fatan Allah Ubangiji ya saka musu da mafificin Aljanna.

Haka zalika ma’aikatar ta kuma yabi gwamnan Zulum da irin goyon baya daya ke baiwa bangaren addini inda aka samu canje-canje masu muhimmanci wanda zai kai ga ci gaban jihar.

Hakanan Hon. Abatcha Umar ya kuma godewa gwamnan jihar Borno na rikon kwarya Umar Usman Kadafur dake tafiya da kowa-kowa.
Ya kuma bukaci al’umman jihar Borno da suyi amfani da damar wajen yiwa jiha addu’an zaman lafiya, hadin kai a jihar Borno da Najeriya baki daya.