
Kungiyoyin yan kwallo kafa na jihar Borno sun kai ziyarar ban girma zuwa ofishin sabuwar sakatariyar wasanni na jiha Hajiya Amina Manga.
Yayin ziyarar, shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Bunu daya jagoranci kungiyoyin ya taya sakatariyar murna kuma ya nemi goyon bayan ta.
Yace kungiyar su tana da kungiyoyi dari uku a karkashin ta kuma ya nemi gwamnati data samar musu da wadatacciyar fili na buga kallo tare da basu tallafa domin horas da mabobin su a gidauniyar wasanni na Najeriya a jihar Laos duk da nufin ciyar da kallon kafa gaba a jihar.

Cikin jawabin ta, hajiya Amina Manga ta godewa masu kungiyoyin kwallon kafar, kuma tayi musu alkawarin kai bukatar su gaban ma’aikatar wasanni da matasa na jiha.
