Kungiyar yan ta’addan Islamic State of Iraq and Syria (ISIS) tace ta kai harare 517 a fadin duniya daga watan janairu zuwa maris.
Kungiyar ta nada kasar najeriya ta biyu inda tace ta samu harare 112.
sauran kasashen dasuka bayyana sun hada da Iraq 162; Syria 106; Egypt 30; Afghanistan 68; Democratic Republic of Congo 18; Niger 9; Pakistan 7; Tunisia 2; Chad 1; Mali 1 da Somalia 1.
Kungiyar Islamic state west African province wadda take karkashin ISIS tace takai harare daban-daban kasar najeriya a cikin kwanaki 81.
Hukumar tsaro ta amurka tace akwai harare da raunuka dama daya afku a kasashen afirka amma afirka ta yamma da sahel sunfi shafuwa.
Hukumar tsaron ta amurka tace kungiyar ta’addan isis takance tana kai harare da dama a afirka ta yamma tun shekara 2014.
Inda kungiyar ta kashe mutane sama da dubu dakuma raba su da muhallan su a yankin arewa maso gabacin najeriya.