
Shahararriyar kungiyar nan mai zaman kanta ta UN-WOMEN ta fara shirin ayyukan wayar da kai a jihohin Borno da Yobe kan cin zarafin jinsi.
Sun fara assasa wan nan ginin da masu ruwa da tsaki a yankin na Arewa maso gabas don dakile ayyukan a yankin na Borno da Yobe.
Haka nan kungiyar tace mata zata taimakawa wadanda suke a yankin da ake fama da rikici da kuma annobar COVID-19.

Acewar Dr. Abiola Akinyode Afolabi babban daraktan shirye shirye yace idan aka taimakawa mata an taimakawa kasa baki daya ne.
Afolabi ya kara da cewa UN-WOMEN na taimakawa wajen karfafawa mata gwiwa ta fanninshiga cikin siyasa, karfaf su wajen tatalin arziki, zaman lafiya, tsaro dama ayyukan bada agaji.
Haka nan Abiola yace ayyukan zasu kawo dokoki da samun hukunta masu laifi dama karfafawa matan damar samun hukuncin day a dace da kuma koya musu ayyuka da gina su ta fanoni a jihohin Borno da Yobe
