Kungiyar Tarayyan Turai Tare Da Kungyar Mercy Corps Sun Bayar Da Gidaje Masu Amfani Da Sola Ga Gwwamnatin jihar Borno.

CollageMaker_20210228_181539990
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar tarayyan turai tare da kungyar Mercy Corps sun mika gidaje masu amfani da wutar sola sama da dari 3 da 25 ga gwamnatin jihar Borno.
Gidajen wanda suke Bama, anyi ne domin komawar yan gudun hijira wanda aka lalata musu mazaunin su .
Shirin gidajen na Mercy Corps wani bangare ne na ayyukan shirin MAIDA na watanni 36 da kungiyar tarayyar turai ta kaddamar kuma ta dauki nauyin ta a watan Desamba na shekarar 2017, yayin mika gidajen a Bama daraktan Mercy Corps na kasa Ndubisi Anyawu yace hadin kan su shine domin samun cigaba mai dorewa da kuma shawo kan kalubalen da aka fuskanta a yankunan da yan ta’adda suka lalata.
Anyawu wanda ya samu wakilcin Raiz Khan yace shuwagabannin al’umma a Bama sun taka rawar gani wajen ginin gidajen haka kuma yace jama’a sun yi kokari wajen samar da kayakin gine gine yayin ginin gidajen a Bama.
Gwamnan Zulum yayi godiya kuma yace gidajen da aka kamala a Gwoza da Bama zai kawo sauki wa yan gudun hijira a sansanoni.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban sakatare na ma’aikatare sake ginawa da maida yan gudun hijira injiniya Abba Ysuf yace gidajen anyi ne domin yan hijira.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply