Kungiyar NYCPSD Sunyi Kira Ga Najeriya Ta Hada Kai Da Kasashen Dake Makotaka Da Ita Wajen Yaki Da ‘Yan Ta’adda

YOUTH COALIATION
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kungiyar matasa ta Coalition of Nigerian Youth for Peace and Development sunce ya kamata a kawo karshen ta’addanci da harkar yan bindiga a kasar ta hanyar kafa jami’an hadin gwiwa da kasashen da ke makotaka dasu.

Kungiyar tayi kiran ne bayan harin da ‘yan ta’addan suka kai jihar Borno da kuma na ‘yan bindiga a jihar Katsina inda suka kashe mutane da dama, dabbobi, da kayayaki.

sun fitar da takardar ne wadda sakataren kungiyar Josiah Useni yasa hannu ya fitar da ita inda wakiliyar mu Yagana Ali in daga Yola ta aiko mana inda sukace yan ta’addar na guduwa su sake kafuwa a kasashen dake maktaka da Najeriya sukai wasu hare-hare.

haka nan sun yabawa gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Zulum da ziyarar da ya kai kauyen Fanduma Kolomdi a karamar hukumar Gubio linda yan kungiyar Boko Haram suka kai hari.

san nan sunyi kira ga jami’an tsaro dasu kai yakin karshe yankin tafkin Chadi wanda zai kawo karshen ta’addanci a yanki.

haka nan sunce akawi bukatar daukar matakin gaggawa na hada manyan garuruwa da kanana.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply