Kungiyar Musulman Tangale Sunyi Kira Da Ayi Bincike Kan Rikicin Billiri

FB_IMG_1613592776435
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar Muslim Tangale dake karamar hukumar Billiri a jihar Gombe sunyi alla wadai da hari da lalata kayan Musulmai da wasu sukayi da sunan zanga-zangar lumana.

Acewar shugaban karamar hukumar Malam Isah Ibrahim a rahoton day a fitar yace ance za’ayi zanga-zangar ne kan gwamnatin jihar ta zama tana karkashin sarakunan gargajiya amma sai abun ya rikide da farwa musulmai da lalata dukiyoyin Musulmai.

Malam yayi kira da ayi gaggawar kama wadanda suka aikata wadan nan laifukan akan Musulmai a garin na Billiri ranar juma’a.

Haka nan yayi kira ga kungiyoyin Musulmai, Kiristoci dana Yeku inda yace dukkaninsu suna bin doka kuma suna da yakinin cewa gwamnatin jihar zata yi musu adalci.

Malam Isah yayi kira ga gwamnatin jihar data taimaka ta biya diyya ga wadanda suka samu asara a shagunan su da sauran hanyoyin kasuwanci saboda ayyukan da wasu daga cikin Kiristocin suka yi.

A nashi bangaren gwamnan jihar yace dokar hana ta fita cikin awanni 24 ya saka ya saka ne saboda bashi da zabi sakamakon rikicin da akayi asarar rayuka da dukiyoyi.

Haka nan yace a yanzu an dakatar da duk wani taron zaben sabon shugaban Tangale a masarautar har sai an samu zaman lafiya a yankin baki daya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply