Kungiyar kwadago Ta Yabawa Gwamna Zulum Bisa Biyan Dukkan Kudaden Mutanen Da Suka Bar Aiki

nlc
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kwadago a jihar Borno ta yabawa gwamna Babagana Umara Zulum bisa biyan kudaden gratuti na wadanda suka bar aiki dubu 4 da dari 8 da 62 na shekarar 2013 zuwa 2017 rayayyu dama wadanda suka rigamu gidan gaskiya.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar kwadagon a jihar Borno Bulama Abiso da takarar sa na kungiyar yan kasuwa Babayo M. Hamma suka mikawa gidan rediyo dandal kura
Cikin sanarwar kungiyoyin sun godewa gwamnan jiha bisa faranta ran wadanda suka bar aikin da yayi kuma suka yaba da halayen sa tare da cewa zasu ci gaba da mara masa baya domin cikar muradin.

gwamnatin sa guda 10 ga jihar Borno
Bulama Abiso ya kara da cewa suna aiki tukuru domin ganin an biya albashin sabbi dama tsoffin wadanda suka bar aikin da zaran an gama tattara bayanan su a na’ura kuma ya roki wadanda aka samu matsala a nasu cea su kasance cikin hakuri.
Gidan rediyo Dandal Kura ta ruwaito cewa gwamna jiha ya sake kudi naira biliyan 12 domin sasanta bashin jama’a.

Kungiyar kwadagon sun kum a yi addu’ar Allah ubangiji yayi ma gwamnan jihar jagora da kuma kariya dama isasshen lafiya da kuma basiran cigaba da jagorar jihar dama yankin baki daya

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply