Kungiyar kwadago reshen jihar Borno ya bukaci gwamnatin jihar da ta sake duba kudin fansho da gratuti da take fitarwa ko wane wata zuwa miliyan 100.
hakan na cikin sakon da ta fitar a shekarar nan a ranar kwadagon wanda shugabanta na jihar Borno kwamared Bulama Abiso ya fitara ofishisu dake Maiduguri.
Comrade Abiso yace hakan zai sa gwamnati ta biya kudaden da tsofin ma’aiktan ke binta a jihar.
ya kuma godewa gwamnan jihar kan fitar da Naira biliyan 12 don biyan ma’aikata.
san nan ya roki gwamnatin jihar da ta tabbatar da biyan kayyadajjen albashi na Naira 30,000ga ma’aikatan kananan hukumomi dama masu aikin ilimi na matakan kana nan hukumomin hade da Karin kudi duk shekara dama Karin girma.
yayin da gwamnan jihar Babagana Zulum wanda shugaban ma’aikta na jihar Mr Simon Malgwi ya wakilta yace gwamnati na kokarin ganin ta cimma burin ma’aikatan duk da yanayi da ake ciki na matsin tattalin arziki.
haka nan gwamna Zulum yace gwamnatinsa ta amince da tsarin komawa cikin yan fansho cikin sauki dama biyan albashi da sauran hakkoki.