
Kungiyar International Organisation for Migration tace an ceto masu hijira ba bisa ka’ida ba su 6,848 inda aka mika su kasar Libya a shekarar 2020.
IOM tace wadanda aka ceto din sun hada da mata 474, yara kanana 364 minors,haka nan sunce mutane 115 sun rasu sai kuma 180 da suka bata a hanyar Mediterranean a wan nan shekarar.
Haka nan sunce gaba daya wadanda aka ceto aka kaisu kasar Libya a shekarar 2019 sun kama 9,225 sai 270 da suka rasu sai kuma 992 da suka bata.

San nan sunce faduwar gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011 ya kawo rashin tsaro da rudani a kasar ta Libya.
Hakan ne yasa kasar take sa masu hijirar bada izini ba da tsallakawa ta kogin Mediterranean a hanyarsu ta zuwa turai.
Wan nan na daya daga cikin dalilan da yake sa ‘yan hijrar ke yawa a kasar Libya aduk da kiran da kasashen duniya keyi na a kulle su.
