
Kungiyar lafiya ta duniya wato WHO tace yara fiye da miliyan 59 ne a Afrika suke a rame inda kimanin miliyan 10 ke da kiba da ta wuce misali.
Haka nan sun gargadi yan Afirika dasu yi kokari su cimma harkar lafiya kafin shekarar 2030, wanda in ba haka ba zasu gamu da matsaloli guda biyu na rashin mutane masu ingantaccen abinci da wadanda kibarsu tayi musu yawa.
Ana samun karancin abincin mai gina jiki ga mutanen da basu da abinda zasu ci wanda hakan yake sa yara su zama a rame. A daya bangaren kuma mutanen da suke da kibar da ta wuce misali na fama da kitsen da yayai musu yawa a jiki wanda hakan zai kawo illla ga lafiyarsu.
Jami’in kungiyar ta WHO a Afrika yace ya kamata a duba wadan nan matsalolin guda 2.
