Kungiyar Kasashen Turai Da Save The Children Sun Fara Rabawa Mata Masu Juna Biyu 10,000 A Jihar Yobe

Kungiya mai zaman kanta ta Save the Children International (SCI), da hadin gwiwar kungiyar kasashen turai ta samar da taimakon kudaden naira 10,000 ga mata masu juna 2 da shayarwa a jihar Yobe.

mai kula da shirin na kungiyar kasashen turai a Yobe, Mr Lawal Tsafe, ya bayyana hakan a Damaturu yayin duba inda ake biyan kudaden.

yace ko wace mai juna 2 da mai shayarwa suna karbar Naira 7,500 tun shekarar 2019.

Haka nan yace tura kudaden da EU take yi tana yi tana yi ne karkashin Save the Children International.

san nan yace yace zau bawa masu ciki 10,000 masu shayarwa kuma N7,500 a kowane wata cikin kwanaki 1,000.
Tsafe yace za’a fara daga farkon ciki zuwa shekaru 2 na yaron.

san nan yace kananan hukumomi 2 ne aka zaba na Damaturu da Postiskum.
ya kuma ce mutane 4000 ne a Damaturu sai 6,000 a Potiskum.

Ya roki wadan da zasu amfana da su yi amfani da kudin don kula da yaran nasu har tsahoon shekarun 2.

Kuma ya Bukace su da su dinga tara kudin don yin dan kasuwanci don dogarao dakai bayan sun dena karbar kudaden.

Wata da ta amfana Gambo Goni, tace kudin na taimaka mata musamman da take da ciki kuma ma’aikatan kiwon lafiya sun bukace ta data dinga cin abinci mai gina jiki.