Kungiyar Iyaye Da Malamai Makarantu Sun Bukaci Asa Tsaro A Makarantu

schools
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar iyaye da malaman makarantu ta kasa ta bukaci gwamnatocin kowane mataki dasu tabbatar cewa sun samar da tsaro a dukkanin makarantun dake fadin kasar.

Shugaban kungiyar Haruna Danjuma ne ya bayyana hakan a rahoton day a fitar a Kaduna inda yace yadda ake kai hari makarantu ake garkuwa da dalibai ya fara zama abun damuwa ga Malami da iyaye.

Danjuma ya kara da cewa ya kamata gwamnatocin kowane mataki su farka kan matsalar tsaron da ake fama da ita wadda ta shafi dukkanin harkokin kasar ciki harda tattalin arziki.

Haka nan yace har yanzu iyaye na cikin tashin hankalin yadda a kwanankin nan aka sace daliban makarantar sakandire a Kagara a jihar Neja.

Kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya data jihar Nejan dasu dage su sasantawa suga an saki dalibai da malaman na makarantar ta Kagara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply