Kungiyar Gwamnonin Najeriya Da Miyetti Allah Sun Tsaya A Matsaya Daya

images (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar gwamnonin Najeriya da kungiyar Miyetti Allah sun amince da rashin kiwon dare da kuma wasu ayyukan da basu dace ba a dazuzzukan dake yankin kudu maso yammacin Najeriya.

A karshen taron da aka gudanar kan sha’anin tsaro tsakanin gwamnonin da yan kungiyar ta miyetti Allah ranar Litinin a garin Akure an tsaya kan inda aka hana dattijai kiwo.

Haka nan kamfanin dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa wamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu, Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, Mohammed Abubakar na Jigawa da kuma Gboyega Oyetola na jihar Osun.

Ragowar sune Gwmna Seyi Makinde na Oyo da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun Senator Iyiola Omisore.

Sai Kayode Fayemi na jihar Ekiti wanda shine shugaban gwamnonin wanda ya karanta dokar inda yace idan aka bar harkar kiwon ba dokoki za’a samu rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Haka nan su rawaito cewa Akeredolu ya bawa makiyayan umarnin barin jihar cikin kwanaki 7 inda yace suna gudanar da kiwon ta haramtacciyar hanya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply