Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas Zasu Samar Da kamfanin Sauka Da Tashin Jirage.

FB_IMG_1614807327340
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas ta bayyana cewa zata samar da kamfanin tashi da saukar jirage a yankin arewa maso gabas da kuma banki domin saukaka da kuma inganta tattalin arziki a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ita ta bayyana cewa kungiyar gwamnonin sun hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe.

Farfesa Babagana Zulum wanda shine shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno ya bayyana haka a taron su domin sake ginawa tare da inganta gidan gwamnati na jihar Bauchi.
Yace yankin yana bukatar gyara sakamakon matsalar ta’addanci.

Ya kara dacewa a baya kasar nan tayi fama da gurbaceciyar gwamnati da matsalar cin hanci, saboda haka lokaci yayi da za’a kawo cigaba a kasar nan

Gwamnan ya cewa kungiyar tayi yunkurin gina filin tashi da saukar jirage da kuma banki a yankin domin saukakawa jama’a a yankin arewa.

Daga karshe yace kungiyar ta shirya kawo sauye sauye a yankin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply