Kungiyar fararen hula da hukumomin tsaro a yankin arewa maso gabas sun taru a Maiduguri domin samar da dabaru zaman lafiya mai dorewa a yankin.

borno state small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar fararen hula da hukumomin tsaro a yankin arewa maso gabas sun taru a Maiduguri domin samar da wasu dabaru na gina zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bukaci masu ruwa da tsaki da su taimaka kuma su bada goyon baya domin wanzar da zaman lafiya wajen farfado da kokarin gwamnatin jihar.

Taro karo na farko da kungiyar fararen hula ta gabatar kan tsaro ya maida hankali ne kan matakan da ya dace, da inganta kyakkyawan alaka tsakanin kungiyoyi daban daban da kuma mai da hankali kan kungiyoyin marasa karfi.

A yanzu haka mutane sama da miliyan 1 suna cikin halin bukata da kuma taimako domin inganta rayuwar su.

Gwamnan jihar Borno wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata na jihar Isa Hussaini yace hadin kai na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas, haka kuma yace zaman lafiya, shugabanci na kwarai sune hanyar cigaba na kowani kasa.

Daga karshe gwamnan ya bukaci kungiyar fararen hulan da kungiyoyi masu zaman kansu da su maida hankali kan karfafawa yan gudun hijira a yankunan su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply