Kungiyar Cigaban Al’ummar Masarautar Jihar Borno Tayi Kira Ga Garba Shehu Daya Bada Hakuri Kan Kalamansa

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar cigaban al’ummar masarautar jihar Borno tayi kira ga mai Magana da yawuun shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sha’anin yada labarai Mallam Garba Shehu day a nemi bawa yan Najeriya da mutanen Zabarmari hakuri kan kalaman da yayi na cewa sun fita gona ba tare da takardar izini ba daga jami’an soji.

Yayin da yake yiwa gidan radiyon dandalkura jawabi shugaban kungiyar Zanna Hassan Zannah Hassan Bogums ya bayyana cewa kalamansa kan mamatan bai dace bay a nuna rashin damuwa da abun day a farun a jihar ta Borno.

Haka nan sunce cewa wai manoman sai sun karbi takarda daga hannun sojoji kafin girbe shukarsu abin takaici ne.

Sun kara da cewa bai kamata a dinga bawa mamata laifi ba a abubuwan da gwamnati ta gaza na kare rayuwar yan kasa.

Kungiyar tayi kira ga shugaba Buhari da zo Maiduguri don ganawa da masu ruwa da tsaki jami’an soji harda wadanda suka bar aiki, sarakunan

gargajiya, maharba, masu sintiri, yan kungiyar CJTF don jin sahihan bayanai kan yakin da ake day an ta’addan a yankin arewa maso gabas.

Haka nan sunyi alla wadai da harin inda Boko Haram suka kashe manoman shinkafa fiye da mutane 50 a garin Koshebe dake karamar hukumar Mafa a jihar ta Borno.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply