
A ranar alhamis kumgiyar al’adun yarbawa suka bayyana goyon bayan su ga kudirin majalisar wakilan kasa na haramta shigowa da hada mayukan bleaching wato rine fata a Najeriya.
Shugaban kungiyar Hammed Olalekan, yayi matukar farin ciki da kudirin hana shigarwar da hada mayukan wanda ake amfani dasu ana rina fata.
Olalekan ya kuma ce yana daga cikin muradin kungiyar tabbatar da kyawawan dabi’u tsakankanin matasan Najeriya kuma yace kingiyar tasu ta YYSA ta bada cikakkiyar goyon bayan ta domin rine fata wani na’ui na rashin tarbiyya ne a Najeriya.

