Kotun ECOWAS Ta Bawa Gwamnatin Najeriya Umarnin Biyan Sojoji 244 Da Aka Kora A Shekarar 2016 Hakkokinsu

ECOWAS
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kotun Kungiyar hadin kan kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ta bawa gwamnatin najeriya umarnin biyan albashi da hakkokin sojoji 244 da aka kora a shekarar 2016.

Kotun ta fitar da rahoton ranar Juma’a inda tace ta bayan an yanke hukunci an bawa gwamnatin umarnin biyan sojojin kudadensu. A baya kotun ta yanke hukunci a watan Mayu na shekarar 2019 inda tace ba’a bi doka ba wajen yankewa sojojin hukunci.

Haka nan kotun tace gwamnatin ta biya su hakkokinsu tun daga watan junairu na shekarar 2016. A hukuncin da mai shari’a Keikura Bangura ya yanke yace kotunta yanke hukuncin bayan taji daga bangarorin biyu.

A koken nasu da suka bayar ranar 14 ga watan Juni na shekarar 2019 da sun bukaci da a maidasu bakin aiki hade da bi musu hakkinsu kan maidasu matsayinsu da mukamansu da kuma hukuncin da akayi musu da farko wanda baya kan ka’ida.

Haka nan sunyi kira da a biyasu hakkokinsu tun daga shekarar of 2015.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply