
Akalla yan kato da gora guda bakwai ne suka mutu a safiyar jiya, bayan su taka wani abin fashewa wanda ake zargin Yan kungiyar Boko Haram ne suka dasa.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kawuri na karamar hukumar Konduga wanda ke kimanin kilomita 37 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.
Gidan rediyon Dandal Kura ya tattaro cewa ‘yan banga suna kan aikin su na yau da kullun lokacin da lamarin ya faru.
Wani ganau ya ce an kai gawarwakinsu asibitin koyarwa na Maiduguri.
Jihar Barno ita ce yankin da aka kwashe shekaru goma an fafatawa da yan boko haram a kasar .
