
Kwamandan yankin jihar bauchi Yusuf Abdullahi na hukumar kare hadura ta kasa wato FRSC yace kimanin mutane 10 ne suka rasu a hadarin daya afku Azare, dake karamar hukumar Katagum .
Abdullahi ya bayyana hakan a hirar da yayi da wakilinmu a Bauchi, inda yace harin ya afku da misalin 2:30 na yamma inda mutum 12 suka samu raunuka.
Ya kuma bayyana cewa wani mashin ne da yadauko mutane 4 yazo ya daki mota kirar bus mallakin Gombe line express inda dukkanin mutanen kan masjhin din suka rasu.
Abdullahi yace 6 kuma sun rasu cikin hayis din inda aka kai gawawwakin Federal Medical Centre, dake Azare.
Yace wadanda kuma suka samu raunin an kaisu asibitin New Jama’are dake Azaredon karbar magani.
Cikin wadanda suka samu raunuka 12 guda 6 maza ne manya sai mata 3 da yaro namiji 1 da yara mata 2.
Haka nan ya danganta hatsarin da gudu mara misali inda yayi kira ga masu motocin hayar dasu su dinga sassautawa yayin tukin.
