Kimanin Dalibai 500,000 Ne Zasu Amfana Da Shirin Koyi Daga Gida A Radiyo

AUN small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rahotanni daga jihar Adamawa na bayyana cewa sama da dalibai dubu dari 5 ne zasu amfana daga shirin koyan karatu daga gida da ake gudanarwa a gidajen rediyo a jihar na Adamawa da Gombe.

Wakilin mu ya shaida mana cewa, kungiyar asusun ilimi na amurka tare da hadin kan gwamnatin jihar ne suka hada kai don karfafa harkar ilimi a jihar wanda kuma jamiar APTI ta tsara.

Mataimakin gwamnan jihar Adamawa Crowther Seth wanda ya wakilci gwamna fintiri yace, gwamnan ilimi shine babban muradin gwamnatin sa.

Haka kuma shugaban jamiar Professor Dawn Dekle wadda farfesa Abubakar Abba Tahir, mataimakin alakar jamioI yace jamiar zatci gaba da fito da tsare-tsare da zai amfanar da marasa galihu da kuma iyalai dake fuskanta matsaloli.

Ta kuma ce a wannan lokaci da annobar Covid 19 ya mayar da komai baya, tana fatan wadanda akayin domin su zasu amfana da shirin koyarwa yadda ya dace.

Tsohon shugaban kasar najeriya kuma wanda ya samar da jamiar turai na najeriya a Yola, Alhaji Atiku Abubakar yace an yi shirin ne don yara dake matakin frimare musamman ma na aji 1 zuwa 3 domin suna mataki mai muhimmanci na daukan karatu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply