Kashi 90 Na Yan Najeriya dake Dauke Da Cutar Coronavirus Zasu Warke – Ministan Lafiya

covid
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya tabbatarwa Najeriya da cewa kashi casa’in a cikin dari na mutanen da suka kamu da cutar corona virus zasu samu lafiya.

Ministan yayi wannan bayani ne a yayin ansa wata tambayar da aka yi masa a bayanin kwamitin kar ta kwanana na yaki da cutar corona virus nakasa.
A daren ranar laraba a kalla mutane dari takwas da saba’in da uku ne suke dauke da cutar ta covid-19 a yayin da kimanin mutane 197sukasamu lafiya kuma har an sallamesu yayin da mutane ashirin da takwas kuwa rai yayi halinsa.
Dayawa daga cikin wadanda suka rasun, mutane ne da suke dauke da wasu cututtka tunkafin kamuwa da cutar.

Kimanin mutane miliyan biyu ne suka kamu da cutar ta covid-19 a duniya sannan kuma a cikin su mutane dubu dari da sittin da tara da dari tara da ar’bain ne suka rasu. Sannan kuma mutane dubu dari shida da ar’bain da biyar da dari da sittin da hudu ne sukawarke.

Mr. Ehanire yace cibiyar yaki da cututtuka masu bazuwa zata rinkagwajin ta ga mutane dubu daya da dari biyar zuwa mutane dubu uku a kowace rana.

Ya kuma kara da cewa hauhawar mutanen da ake samu masu dauke da cutar ana samunsu ne sanadiyar kara fadada yawangwajin da akeyi domin kokarin dakile bazuwar cutar.

Mr. Ehanire yace duk wani matafiyi da zai shigo Najeriya se an tabbatar an killace shi harna tsawonkwanaki goma sha hudu domin a kaucewa shigowa da cutar daga wasu kasashe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply