Kasar Tanzania Ta Fara Buga Wasan Laliga

Tanzania
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A wan nan satin makon kasar Tanzania ta fara gudanar da wasannin laliga bayan da ta dakatar da wasannin a watan Maris sakamakon annobar coronavirus.

Tanzania ta dakatar da wasannin na club 20 tun a watan na Maris kan COVID-19 wadda ta fara durkushe kasashen Africa.

Acewar Africa Centre for Disease Control ranar 13 ga watan Juni Afrika nada mutane 225,126 inda mutane 6,051suka rasa rayukansu.

An bar yan kallo yayin da aka fara wasannin amma banda tsofaffi da yara wadanda ake ganin su zasu fara kamuwa da cutar.
Haka nan kafin a barka ka shiga sai kasaka takunkumin fuska, ka wanke hannu kuma an duba yanayin zafin jikinka. Haka nan idan ka shiga dole ka bada tazara.

San nan yan kwallon da masu busa, da kuma masu hararwar na daukan matakai na yin feshi kafin da kuma bayan ko wane wasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply