Kasar Saudi Arabia Tace Zata Kayyade Mutanen Da Zasu Gudanar Da Aikin Hajjin Bana

saudi arabia
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kasar Saudi Arabia tace zata kayyade mutanen da zasu gudanar da aikin ahjjin bana da muatne dake cikin kasar kadai wanda za’a fara karshen watan Yuli.

Sakamakon annobar COVID-19 da ake samu a kulllum a duniya baki daya kasar ta Saudi Arabia zata kayyadade muatnen da zasu gudanar da aikin hajjin na Bana gay an kasar dake zaune acan kadai.

Ma’aikatar aikin Hajjin da Umrah ranar litini ta bayyana cewa an yanke hakan da bin ka’idoji kamar bada tazara tsakanin mutane, da kuma kare rayukann mutane kamar yadda addinin musulunci ya umarta.

Har yanzu dai ba’a tabbatar da mutane nawa ne zasu gudanar da aikin Hajjin ba. Fiye da mutane miliyan biyu ne suke gudanar da aikin Hajjin a kowace shekara daga kasashe daban-daban a garin na Makka.

Haka nan ana gudanarshi na kwana 5 daga 8 ga watan Dhu al-Hijjah zuwa 12 ga wata na karshen watan Musulunci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply