Kasar Najeriya Zata Karbi Bakuncin Yan Kasuwan Afrika Domin Taron Duniya A shekarar 2021.

images (6)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba mai lura da zuba hannun jari a kasuwannin Afrika a taron duniya Angelo Elosia yace kasar Najeriya zata karbi bakwancin yan kasuwan duniya domin hade kasuwannin duniya waje guda wanda za ayi a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2021.

Ya bayyana haka ga manema labarai kan bangaren zuba jari a Afrika a taron duniya na wannan shekara kan tattalin arziki a Afrika.

Yace taron zuba hannun jari aAfrika wani shiri ne na canjin yanayi wanda ake sa ran zai tara yan kasuwa na duniya a Afrika a shekarar 2021 wanda aka mata taken “Economic and Technical Innovations for Africa During and After COVID-19.

Yace manufar wannan shirin shi ne domin hada kan kasashen Afrika wuri guda.

Haka kuma manufar su wanda ya fara tun shekarar 2003 shine domin hada kan shuwagabannin kasashe, masu ruwa da tsaki da masu zuba hannun jari na kasa da kasa domin farfado da tattalin arziki da daurewar alaka.

Cikin wadan da suka halarci taron akwai manyan jami’ai a gwamnati, masu ruwa da tsaki da masu zuba hannun jari na kasa da kasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply