Kasar Najeriya Ta Samu Karin Sabbin Masu Cutar corona virus.

images (17)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kasar Najeriya ta samu sabbin karin masu cutar corona daga dari 8 da 29 zuwa dari 8 da 38.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa ne ta bayyana haka a ranar Lahadi a shafin tan a Twitter.

Rahotan da aka fitar a jiya Lahadi ya nuna cewa babban birnin tarayya ta samu sabbin masu cutar da suka kai dari 2 da 79 sai kuma jihar Legas da ta samu mutane dari 2 da 53.

Jihar Filato tana da 82, sai kuma Kaduna 57, Katsina 32, Nasarawa 31, Kano 25 sai kuma Gombe 24.

Sauran jihohin sun hada da Oyo da Rivers da suke da mutane 8 kowannen su, Zamfara-7, jihohin Ogun, Bauchi, da kuma Edo suna da mutane 4 kowannen su, sai kuma jihohin Anambra da Sokoto da suke da mutane dai daya.

Ya zuwa daren ranar Lahadi kasar tana da wadanda suke da cutar corona da suka kai dubu 84 da dari 4 da 14 sai kuma an salami dubu 71 da 34

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply