Kasar Indonesia Ta Soke Aikin Hajji Na Wan Nan Shekarar

makkah
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan harkokin addini na kasar Indonesia Fachrul Razi ya tabbatar da soke aikin Hajji na wan nan shekarar.

Fachrul ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da amanema labbarai a Jakarta inda yace gwamnati ta soke hajjin banan sakamakon rashin tabbas daga kasar ta Saudi Arabia.

Ministan ya bayyana cewa sun yanke wan nan hukuncin bayan tunani da sukayi kan kare lafiyar jama’a sakamakon annobar Cornavirus da ake fama da ita a fadin duniya.

Fachrul ya bayyana cewa suna fata ayi hajjin shekara mai zuwa, Kasar Indonesia nada kaso mafi girma na mutane da suke zuwa hajjin.

Haka nan kasar Singapore itama ta bayyana cewa yan kasarta baza su gudanar da aikin Hajjin na wan nan shekarar saboda annobar coronavirus.

Dandal Kura Radio ta gano cewa Najeriya zata bayyana nata hukuncin idan sun gama tattaunawa da kasar Saudi Arabia.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply