Kasar India Zata Fara Jigilan kawo Rigakafin Corona Ma Kasar Nijeriya.

flag-of-india
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban jakadan India a Najeriya Mr Abhay Thakur yace kasar sa zata cigaba da yin jigilan magungunan kariya na Corona virus bayan sun gama tattaunawa da hukumomi a Najeriya a wannan mako.

Mr. Thakur yayi wannan jawabi ne a wani taron yan India zalla karo na 16 da akayi a Najeriya.

Babban Jakadan yace za a kawo magungunan kariyan ne daga lokaci zuwa lokaci ya danganta da tattaunawar su da hukumomi.

Yace zasuyi farin ciki idan suka samar da rigakafin bisa tsarin gwamnatin Najeriya ko kuma bukatar da ta tsara.

Ya kara dacewa sunyi kokari matuka ba lokacin cutar Corona kadai ba har lokacin bullar cututtuka da dama da kuma taimakon da suka yiwa Afrika kan magungunan cutar AIDS

Yace hakan zai kara karfafa alakar dake tsakanin kasar India da Najeriya inda yace jama’ar India a Najeriya sun taimakawa Najeriya kwarai kan yaki da cutar Corona.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply