
shugaban kasan china xi jinping ya fitar da sanarwa cewa kasar sa, zata taimakawa nahiyar africa da kudade kimanin dalar amurka biliyan 60.
yayi jawabin hakan ne yayin taron kolin beijing tsakanin nahiyar africa da kasar sin da zummar taimakawa kampanonin nahiyar.
ya kara da cewa kasar sa zata kebe wasu kasashe, da suke fama basussuka sannan hakan zai gudana a kasashe marasa karfin tattalin arziki masu hulda da kasar.
haka zalika yace zai kaddamar da wasu manyan aiyuka akalla 8 a nahiyar afrika a cikin shekaru 3 masu zuwa
