Kasar Burtaniya zata ware Miliyan Ar’bain Da Bakwai Domin Tallafawa A Bangaren Abinci da kuma ,Ruwan Sha. , .

Seal_of_the_United_States_Africa_Command.svg
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kasar Burtaniya zata ware iro milliyan ar’bain da bakwai domin agazawa a bangaren samar da abinci ,ruwa, da kuma matsugunai ga marasa galihu a kasashe tare da yankunnan su.

An bayyana cewa kasar zata warewa kasar najeriya iro bakwai ta hannan hukuma mai zaman kanta ta World Food Programme inda ana sa ran kudin zai samar mutane dubu darihudu da talatin abinci ingancecce na tsawon kwanaki dari da tamanin.

Hakkan na kunshe ne acikin wata sanarwar da mataimakin shugaban hukumar kasar Burtaniya ya bayar.

Sanarwar ya bayyana cewa bangaren da kasar zatayi aiki akai sun hada da bangaren Abinci,gina jiki,ruwan sha,rigakafin yara, matsugunai da dai sauransu.

Kasar tayi kira ga sauran hukumomin da suma su kawo agaji tare da yin kira ga yan tada kayar bayan da su bada dama domin ganin kayakin agajin ya kai ko ina mussamman wajajen da hukumomin bada’a agaji basa iya shiga.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply