
Kwamitin fadar shugaban kasa kan cutar Korona tace kasar Najeriya a shirye take da ta karbi rigakafin cukat Korona miliyan 1 da digo 4 wanda kamfanin sadarwa na MTN ta bada tallafin sa.
Yayin da yake magana a wajen taron a Abuja, ministan lafiya Dr Osagie Ehanire yace za’ a kawo kashi na farko na rigakafin a karshen watan nan, sannan sauran za’a kawo a karshen watan Maris na wannan shekara.
Haka kuma ministan ya bayyanawa kwamitin assasa rigakafin na Afrika cewa za’a kawo rabin rigakafin AstraZeneca a karshen watan nan wanda kamfanin sadarwa na MTN ta bada miliyan 7 ga Afrika.

Haka kuma ministan ya bayyana wani tallafin na rigakafin dubu dari 1 daga gwamantin kasar Indiya wanda babban jakadan kasar ya bada a matsayin kyauta ga kasar Najeriya daga makarantar Serum na Indiya.
Ministan yace kwamitin kan rigakafin cutar Korona tare da hukumar kiwon lafiya mataki na farko sun tsara hanyoyin da za’
