Kamfanin CCGC Tace Zata Kammala Hanyar Maiduguri zuwa damaturu.

road
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kamfanin Chinese Consortium and Geophysical Construction tace zata kammala hanyar Maiduguri zuwa damaturu mai kilomita 132 a jihar borno.

Hanyar kano zuwa Maiduguri an kaddamar da ita a shekara ta 2005 a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo domin hada sauran jihohi da al’umma don zuwa arewa maso gabacin najeriya.

Sauran kilomita 40 na hanyar daga jakana zuwa Maiduguri, ba’a kammala ba sakamakon bata manyan machinan aikin guda 8 da yan boko haram suka bata a watan afrilu na shekarar 2018.

Shekarar data wuce yan ta’addan sun kai hari kan hanyar inda sukayi garkuwa da matafiya da wasu yan garin.

A dai-dai lokacin sun sake kaiwa hari inda sukayi garkuwa da mutane 45 a kan hanyar.

Bayan shekara 3, kamfanin na china ta koma jakana domin cigaba da karasa hanyar a watan fabrairu na shekarar nan.
Daya daga cikin ma’aikacin wanda yaso a sakaye sunansa jiya a gun gyaran hanyar kusa da Maiduguri, ya bayyana cewa sauran kilomita 40 wanda hanya ce ta shiga babban birni jihar zai kammalu cikin shekarar nan.

Ya umarci mutane da su cigaba da hakuri, saboda jinkirin rashin hanyar ya affku ne sanadiyar matsalan ta’addanci inda aka rasa rayuka da dukiyoyi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply