Kakakin Majalisar Jihar Borno Yace Karamar Hukumar Guzamala Na Karkashin Iko Kungiyar Boko Haram .

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kakakin majalisar jihar Borno Honorable Abdulkarim Lawan ya kalubalanci furuci da ministan labaru Lai Mohammed da tsohon shugaban tsaron kasa janar Gabriel Olonisakin sukayi na cewa rundunar soji sun karbe dukkan kananan hukumomin jihar Borno 27 kuma na karkashin ikon su.

Abdulkarim Lawan yayin taron masu ruwa da tsaki na karamin hukumar Guzamala ya bayyana cewa har ila yau kungiyar Boko Haram na iko da karamar hukumar Guzamala wanda ya kasance mahaifar sa wanda hakan ya tilasta jama’a kasancewa a sansanonin yan gudun hijira na tsawon shekaru.

Yace ya nemi bukatar a zuba rundunar soji a karamar hukumar domin amfani da damar sake gine-gine da gyrare-gyare da gwamnan jihar keyi, sai dai hakar sa bata cimma ruwa ba kasancewar har yanzu babau damar shiga garin.

Kakakin ya roki sabbin shuwagabbain tsaro wanda janar Leo Irabor ke jagoranta da suyi iya kokari su samar da zaman lafiya a karamar hukumar Guzamala domin jama’arsa su ci gaba da gudanar da rayuwa a yankin su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply