Jirgin Max Air Ya Bawa Fasinjoji Hakuri Kan abinda ya Faru A Kano

Max Air, wani kamfanin jigilar jiiragen sama mai zaman kansa, ya nemi afuwar dukkan fasinjojin da ke cikin jirginsa na Boeing 737 kan wani abin da ya faru a Kano ranar Talata.

Mista Harish Manwani, Babban Daraktan Kamfanin Max Air, ya nemi afuwar yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Babban daraktan, wanda ya yaba wa kwararrun kamfanonin jiragen saman kan hanzarin da suke yi don aiwatar da ingantaccen aiki a jirgin sama don magance abin da ya faru, ya kara da cewa irin wannan matakin ya kauce wa wasu abubuwan da ka iya faruwa.

Yace Lamarin wanda ya faru a kan tashin jirginsu mai kirar Boeing 737 daga Kano dauke da manyan fasinjojin da ke jirgin sun hada da Sarkin Kano, da tawagarsa da kuma manyan jami’an kamfanin Max Air ya tashi inda daga bisani injinan ya fuskancimatsala, wanda har yasa matukin jirgin ya dawo da jirgin a hankali a filin jirgin saman Kano.

Ya ce injiniyoyin Air Max sun tantance barnar da wukaken jirgin suka samu wanda kuma suka maye gurbinsu da wasu kamar yadda ya dace.