Jihar Yobe Ta Shirya Dabaru Da Sojoji Da Hukumomin Tsaro Wajen Yaki Da Yan Kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin jihar Yobe ta shirya dabaru da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin yaki da yan kungiyar Boko Haram wanda suka lakume rayuka da dukiyoyin jama’a.

An bayyana dabarun ne a Damaturu babban birnin jihar Yobe a cikin sanarwa wanda aka fitar a taron hadin guiwar majalisar tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

Sanarwar wanda mai bada shawara ga gwamnan kan tsaro janar Dahiru Abdulsalam ya sanyawa hannu, ya bayyana babu abin da ya fi muhimmanci ga gwamnan kamar tabbatar da tsaro da lafiyar jama’ar garin Geidam da sauran sassa na jihar.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki, manyan jami’an gwamnati daga bangaren zartarwa da yan majalisu, sarakunan gargajiya shuwagabannin kansiloli da wakilan yan sanda, hukumar tsaron farin kaya da kuma sashen tsaron farin kaya.

Yace sojoji da sauran hukumomin tsaro da yan banga da kuma masu sa kai kamata su hada kai domin kare garin Geidam da sauran yankuna.

Yace hakan zai sanya mutanen da suke tsere komawa gidajen su.

Daga karshe ya bukaci jama da suyi amfani da wannan daman a watan Ramadana wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya.