Jihar Yobe Ta Dauki Mutane Marassa Galihu 920 A Fannin lafiya.

yobe mai mala
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ma’aikatar lafiya ta jihar yobe ta dauki mutane marassa galihu 920 bangaren sashin lafiya a jihar.

Dr. Muhammad Lawan Gana, ne ya bayyana haka yayin da yaje duba karamar cibiyar kiwon lafiya dake Gwange.

A bayaninsa, yace, an gudanar da shirin ne domin tabbatar da cewar marassa galihu nada hanyoyin samun kulawa ta fannin lafiya.

Ya kara da cewa, tsarin da shirin ya kunsa, shine a ziyarci marassa galihun a yankunan su domin sa su shirin na kiwon lafiya.

Yace, wadanda aka dauka zasu ci moriyar abun ta fanni haihuwa, hanyoyin hana cuttutuka masu yaduwa da kuma maganin jinyoyi da dai sauran su.

Ya kara da cewa mutanen zasu ci moriyar abubuwa ta fannin kiwon lafiya inda jinyar su ta fi karfin karamar cibiyar kiwon lafiya na yankunan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply