
Hukumar Rukunin Masana’antun Dangote ta dage cewa an sayi kamfanin siminti na Obajana a shekarar 2002 bisa ka’ida da tsarin doka, sabanin ikirarin da gwamnatin jihar Kogi ta yi.
Rukunin Kamfanin na Dangote ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ba ta da wani hannun jari a kamfanin siminti na Obajana.
Har ila yau, kamfanin ya bayyana cewa, a matsayinsa na mai bin doka da oda, yana biyan haraji da sauran kudaden da ake biya a jihar ga gwamnatin jihar Kogi tun daga shekarar 2007 lokacin da aka fara samar da siminti a kamfanin.
Wadannan bayanai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mahukuntan Rukunin Masana’antun Dangote suka fitar mai taken ‘Kamfanin Simintin Dangote: Banbancewa Tsakanin Karya da Gaskiya’.
A cewar sanarwar, “Wannan sanarwa ce da aka fitar domin kawai warware damuwa da fargabar masu ruwa da tsaki na kamfanin Simintin Dangote (DCP) musamman ma’aikata sama da dubu ashirin da biyu da suke aiki kai tsaye a kamfanin, da ma karin wasu da suke yiwa kamfanin aiki daga wajen kamfanin, da dubban ‘yan kwangila, da dillalai, da masu amfani da simintinmu, da masu samar mana da kudade, da masu hannun jari.
Kamfanin yace “A daidai lokacin da muke fuskantar gagarumin kalubalen tattalin arziki a matsayinmu na kasa, mun yi amannar cewa dole ne a yi duk mai yiwuwa don ganin an ci gaba da tafiyar da tattalin arzikin kasarmu kamar yadda ya kamata, mutanenmu su samu aikin yi, sana’o’in da suka dogara da mu suna bunkasuwa kuma kada a karya gwiwar masu daukar kasadar saka jarin da ake bukata na halal a tattalin arzikinmu. Rufe masana’antar mu ya kawo cikas ga tattalin arzikin kasarmu ba tare da la’akari da gagarumar illar hakan ba.
Rukunin kamfanin ya kara da cewa, “A yayin da muke amfani da ‘yancinmu na ci gaba da sasantawa bisa ga yarjejeniyar da aka cimma, mun bayar da rahoton mamayar da gwamnatin Kogi ta yi ba bisa ka’ida ba, da kuma illar da hakan ya haifar ga dukkan hukumomin da abin ya shafa, ciki har da gwamnatin tarayyar Najeriya wacce a yanzu ta sa baki a lamarin. Muna fatan tsarin warware rigingimun da muka assasa zai gaggauta warware takaddamar tare da ba mu damar mayar da hankali kan harkokin kasuwancinmu, ba tare da wata tangarda ba, tare kuma da ci gaba da bayar da gagarumar gudunmawar da muke bayarwa ga tattalin arzikin kasa. A saboda haka ne muka bayyana a takaice kamar haka”.
A cewar sanarwar, “Kamfanin simintin na Obajana na daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki a kasar nan, kasancewarsa daya daga cikin kamfanoni masu biyan haraji, kuma jigo a daya daga cikin manyan kamfanoni da dubban masu zuba jari na Najeriya da na kasashen waje suka zuba jari. Muhimman kadarorinsa sun hada da (na 1) filin kamfanin, masana’anta da injinan da ke ciki, da (na 2) dimbin ma’adinan farar kasa wacce kamfanin ke da izinin haka da ya samu a karkashin lasisin gwamnatin tarayyar Najeriya.”
Rukunin kamfanin ya fayyace cewa filin da aka gina kamfanin siminti na Obajana, Rukunin Masana’antun Dangote (DIL) ne kadai ya mallaka a shekarar 2003. “Filin da aka gina kamfanin simintin Obajana, rukunin masana’antun Dangote (DIL) ne shi kadai ya mallaka a shekarar a 2003 bayan ya saye hannun jari a Kamfanin Siminti na Obajana a shekarar 2002, biyo bayan yarjejeniyar doka da ta kulla da gwamnatin jihar Kogi na zuba jari a jihar Kogi. An bawa rukunin masana’antun Dangote takardar shaidar mallaka guda uku da sunan kamfanin bayan ya biya kudaden da ake bukata da kuma biyan diyya ga masu filayen.
Rukunin kamfanin ya yi bayanin cewa, “rukunin masana’antun Dangote ne ya kirkira, ya tsara, ya shirya, ya sayo komai, ya gina, ya biya kudi, bayan ya mallaki hannun jarin kamfanin siminti na Obajana. Farar kasa da sauran ma’adanan da kamfanin siminti na Obajana ke amfani da su, bisa tsarin mulkin Najeriya, mallakin gwamnatin tarayya ne, kuma bayar da lasisin hakowa ikon gwamnatin tarayyar ne kadai ba na jihar da ma’adinan suke ba”.
Sanarwar ta kara da cewa “bayan yarjejeniyar da gwamnatin jihar Kogi, rukunin masana’antun Dangote ya nema kuma ya samu izinin hakar ma’adinan daga gwamnatin tarayya, akan kudin da ta nema, kuma ya kiyaye da ka’idojin izinin tun daga farko. Gwamnatin Jihar Kogi ba ta da ma’adinai ko kadarar da za ta bayar sai dai ta gayyato rukunin masana’antun Dangote kamar yadda mafi yawan gwamnatocin da suka san ya kamata su ke yi, domin zuwa jihar ya zuba jari ta yadda za a samar da ayyukan yi, da bunkasa jihar, da kuma samun haraji”.
A wani sashe na sanarwar mai taken, ‘Kafa Kamfanin Siminti na Obajana da Gayyatar Gwamnatin Jihar Kogi’, kamfanin ya bayyana cewa, “A shekarar 1992, gwamnatin jihar Kogi ta kafa Kamfanin Siminti na Obajana (OCP) a matsayin kamfani mai iko da kansa daidai karfinsa. A wani lokaci a farkon shekarar 2002, kimanin shekaru 10 bayan kafa kamfanin siminita na Obaja (wanda har yanzu lokacin ba shi da wata kadara kuma bai fara aiki ba), gwamnatin jihar Kogi ta gayyaci Rukunin Masana’antun Dangote (DIL) da su ci gajiyar dumbin ma’adanan dake jihar ta hanyar kafa kamfanin siminti a jihar.
Haka nan yace “Bayan tattaunawa daban-daban da kuma tantance yuwuwar wannan damar da ake shirin samu, Rukunin Masana’antiun Dangote (DIL) ya amince da cewa zai kafa kamfanin siminti a jihar Kogi tare da samar da dukkanin kudaden da ake bukata domin kafawa.
Sanarwar ta yi bayanin cewa “DIL ya kuma amince, bayan wata bukatar da gwamnatin jihar Kogi (KSG) ta yi, na yin amfani da sunan OCP (duk da cewa hakan kawai a takarda ne a wancan lokacin, kuma ba tare da wata kadara ko fara aiki ba) na dan wani lokaci, a matsayin ginshikin saka wannan hannun jarin. A ranar 30 ga watan Yuli, 2002, KSG da DIL sun kulla yarjejeniya mai mahimmanci domin rubuta abubuwan da aka cimma. An yi wa yarjejeniyar kwaskwarima a shekarar 2003 kuma tana ci gaba da aiki, kuma a bisa doka, bangarorin da ke da hannu a ciki za su aiwatar da su,”
Dangane da batun wata yarjejeniya tsakanin Dangote da gwamnatin jihar Kogi, sanarwar ta yi takaitaccen bayani, inda ta yi nuni da cewa, “an amince da cewa: DIL zai kafa masana’antar siminti mai karfin samar da siminti tan 3,500,000 a kowace shekara; DIL zai rike kashi 100 bisa na hannun jari a OCP, da kuma samar da dukkan kudaden da ake bukata domin gina kamfanin siminti; KSG za ta samu zabin samun kashi 5 bisa 100 na hannun jarin OCP a cikin shekaru 5; kuma KSG za ta ba da sassaucin haraji da dauke nauyin biyan wasu kudaden da ta ke karba na tsawon shekaru bakwai (7) daga ranar da aka fara aikin samar da simintin.”
Sanarwar ta kara da cewa “Bisa tanadin ka’idojin yarjejeniyar, DIL ta samo kashi 100 bisa 100 na kudaden da aka yi amfani da su wajen gina masana’antar ba tare da wata gudumawa daga KSG ba. Bisa sharadin hakkokinsa, domin tabbatar da daidaito da tsarin kamfanin Dangote, a wani bangare na sake fasali da karin sanayya a kasuwa, an canza sunan kamfanin OCP zuwa kamfanin simintin Dangote a shekarar 2010, sannan wasu manyan kamfanonin siminti (kamar kamfanin simintin Binuwai) mallakin DIL, an hade su da OCP inda suka zama babban kamfanin simintin Dangote”.
Dangane da batutuwan da suka shafi ‘Aiwatar da yarjejeniyar: Ginin Kamfani, Haraji, Hannun jari & Riba’, sanarwar ta kara da cewa, “DIL ba tare da wata miskila ba, kuma a farashi mai yawa ya cika dukkan sharuddan yarjejeniya tsakaninsa da KSG dangane da OCP. Ya gina masana’antar simintin, mafi girma da kyau fiye da yadda ake tsammani.
Kamfanin ya kuma tabbatar cewa: “KSG ba za ta iya cika nauyin da ya rataya a wuyanta na kudin gudummawa wajen samar da tallafin kamfanin ta kowace hanya ba; Haka kuma KSG ba za ta iya samun kudaden mallakar kashi 5 bisa 100 na hannun jarin OCP ba, lokacin da aka neme ta a lokuta da dama domin ta saya.
Haka nan yace “KSG kuma ba ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta ba na ba hutun biyan kudaden da za ta iya karba kan ayyuka da al’amura da harkokin OCP. Maimakon haka duk da cewa kamfanin yana da dama (bisa tanadin sharuddan yarjejeniya da KSG) na sassaucin haraji da hutun biyan wasu kudade da KSG ke karba na tsawon shekaru bakwai (7) daga ranar da aka fara samar da siminti, OCP (wanda a yanzu ya koma DCP) ya biya dukkan haraji da kudaden da ake karba ga KSG tun lokacin da ya fara samar da simiti a shekarar 2007.
Sanarwar ta kara da cewa “KSG ba ta da wani nau’i na hannun jari a kamfanin OCP, don haka ba ta da wata riba ko wasu hakkokin tattalin arziki ko hakkin mallakar dukkan abin da zai iya samu daga ayyukan kamfanin”.
Dangane da batun Sayen Filin Gina Kamfanin, sanarwar ta bayyana cewa, “Bayan yarjejeniyar da aka yi tsakanin DIL da KSG a shekarar 2002, DIL a shekarar 2003, ya rubuta takardar bukata ga KSG ta ba shi filin da za a gina kamfanin, kuma an amince da bukatar ta hanyar bayar da takardun izini guda uku ga DIL. Kamfanin DIL da sanin KSG, ya biya diyya mai tsoka ga masu gonakin Obajana dake filin gina kamfanin mai fadin kilomita murabba’i biyu (2).
Sanarwar ta kara da cewa “Daga baya, a cikin watan Satumbar shekarar 2004, DIL, bisa kyakykyawar niyya, ya rubuta takarda ga Gwamnan Jihar domin nemawar kamfanin DIL izinin bayar da filin kamfanin ga OCP, kasancewar shine ginshikin saka hannun jarin DIL. Gwamnan jihar ya amince da wannan bukatar kuma DIL ya biya kudaden da suka dace,” .
Da take karin haske kan alakar kamfanin da gwamnatin jihar Kogi, sanarwar ta bayyana cewa, “Saka hannun jarin DIL a jihar Kogi ta hannun OCP karkashin umarnin gwamnatin jihar Kogi wadda aka kafa bisa ka’ida, ya kasance bisa tanadin dokokin jihar da dukkan dokokin da suka ba da damar yin hakan, kuma takardun hada-hadar an samar da su yadda ya kamata, bisa ka’ida dauke da sa hannun Gwamna da Babban Lauyan Jiha (na lokacin), bayan an samu amincewar cikin gida a cikin gwamnati.
Sun kuma bayyana cewa “Tun da aka kafa gwamnatin Alhaji Yahaya Bello a shekarar 2016, kuma ba tare da la’akari da cewa ayyukan gwamnati dorawa suke ba, mun sha fuskantar bincike akai-akai game da tsarin mallakar kamfanin simintin Dangote dangane da zargin da ake yi na hannun jarin KSG; an kuma tattauna da jami’an gwamnatin jihar da suka hada da Gwamna Yahaya Bello. A dukkan wadannan zaman tattaunawar mun bayar da cikakkun bayanai bisa goyon bayan takaddun da suka dace, wanda gwamnati da Majalisar Dokokin Jiha ke bukata don tabbatar da saka jarinmu na halal.
Haka nan sunce “Misali, a shekarar 2017, kwamitin bincike na shari’a ya gayyace mu, kuma mun mika wa kwamitin takardun da suka dace domin goyon bayan matsayarmu. Har yanzu ba mu sami amsa daga kwamitin bincike na shari’a ba. A yayin da muke jiran jin rahoton binciken, Majalisar Dokokin Jihar ta gayyace mu kan wannan al’amari a farkon wannan shekarar, kuma mun sake ba da hujjojin da ke tabbatar da matsayinmu na cewa KSG ba ta da wani hannun jari a kamfanin OCP ko DCP.
Sun kuma kara da cewa “A ranar Laraba 5 ga watan Oktoba, 2022, daruruwan mutane dauke da muggan makamai, ba jami’an tsaro ba, sun kai hari a kamfanin simintinmu da ke Obajana, jihar Kogi, suka lalata mana gine-ginen mu, suka yi ji wa ma’aikatanmu da dama mummunan raunuka, tare da dakatar da ayyukan da ake yi a masana’antar. KSG ta amince cewa maharan sun yi aiki ne da umarnin da ta bayar, da kuma ci gaba da binciken da majalisar dokokin jihar Kogi ta yi a kwanan baya dangane da mallakar kamfanin siminti na Obajana.
Haka nan sunce “Abin mamaki, a ranar 6 ga Oktoba, 2022, kwana guda bayan rufe ginin kamfanin mu da ke Obajana bisa umarnin KSG, Gwamna Bello ya yi jawabi ga jama’a tare da sanar da cewa kwamitin fasaha na musamman wanda aka kafa a matsayin wani bangare na shawarar da Hukumar Shari’a ta bayar, ya gabatar da shawarwarinsa, wadanda KSG ta amince da su. Wannan bayanin ya bayyana karara cewa rufe kamfanin na DCP ya faru ne ba tare da la’akari da tabbacin da Gwamnan ya bayar cewa har yanzu ana jiran a fara aiwatar da shawarwarin Kwamitin Fasaha na Musamman”, in ji sanarwar.
Da yake mai da hankali kan halin da ake ciki a halin yanzu, rukunin kamfanin ya ce, “Duk da cewa ba ma son yin hasashe kan dalilan da suka sa KSG ke yin zagon-kasa dangane da mallakar kamfanin, wanda ta yi sanadin rufewarsa ba bisa ka’ida ba, da lalata kamfanin, da raunata mutane da dama, muna yin Allah wadai da kakkausar murya, bisa yadda ‘yan ta’addan da gwamnati ta dauki nauyi suka rufe masana’antar mu ba bisa ka’ida ba, da barnar da aka yi mana (ciki har da wawashe makudan kudade da aka ajiye a ofis) , da kuma mummunan rauni da suka yiwa ma’aikatan mu.
Haka nan sunce “Wannan katsewar aikin da aka samu a masana’antar ya jawo asarar kudaden shiga, ba ga kamfaninmu da kwastomominsa kadai ba, har ma ya haifar da illa ga kudaden shiga ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, ya kuma haifar da asarar ayyukan yi ga matasa masu yawan gaske wadanda ake biya kowace rana, wadanda ke tururuwa zuwa masana’antar mu don samun abincin yau da kullun.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna rokon dukkanin masu ruwa da tsaki da suka hada da masu hannun jari, da kwastomomi, da masu samar da kaya, da ma’aikata, da daukacin al’ummar Obajana da Jihar Kogi baki daya, da su kwantar da hankulansu yayin da muke bin hanyoyin doka da oda domin warware wannan takaddamar. Za mu ci gaba da yin bayani akai-akai ga masu ruwa da tsaki na kamfaninmu kamar yadda ya kamata, yayin da muke da kwarin gwiwar cewa shari’ar da muka shiga za ta tabbatar da hakkokin doka da na kwangila na kamfanin DIL.
