
By: Fatimah Idris Danjuma, Bauchi
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da amincewar sake kudi naira miliyan 5 domin biyan kudaden jinyan marayu da yara masu bukata a fadin jihar.
Gwamnan jihar Bala Muhammad ne ya sanar da hakan yayin rabiyar kayakin kariya ga mabukata 200, ya kuma kara da cewa gwamnatin zata dinga bada kayan abinci ko wani wata ga kananan hukumomi 20 na jihar cikin kokarin san a sama musu ababen more rayuwa.
Gwamnan yace yaji dadin kasancewa wajen gabatar da kayayyakin kuma yace kudaden zasu taimaka matuka wajen warware matsalolin

Dr ladan salihu daya wakilce sa yace koyar da sana’o’in zai tallafa wajen yaye talauci, kuma anba kowannen su naira dubu 10 matsayin mafari
sannan gwamnan ya taya wadanda suka ci gajiyar murna tare da cewa su tabbata sunyi amfani dashi wajen karfafa kawunan su
Sauran da sukayi jawabi yayin taron sun hada da uwargidan gwamnan hajiya Aisha Bala Muhammad da kuma sugaban kngiyar Mrs Hassan Arkilla
