
Jam’iyyar PDP ta ce ba ta ware tikitin takarar shugaban kasa a 2023.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP ta kasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana hakan yayin da ya yi watsi da wasu jita-jita.
An jawo hankalin jam’iyyar ne bisa wasu ce-ce-ku-ce daga wasu mutane da ke ikirarin cewa jam’iyyar ta ware tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a wani yanki na kasar nan.
Wannan lamari ne da ba gaskiya bane domin ba ya wakiltar matsayin jam’iyyar.
Olugunagba ya ce PDP jam’iyyar siyasa ce da aka kafa bisa ka’idojin dimokuradiyya kuma duk wani mataki na jam’iyyar da ya hada da shiyya-shiyya, ya dogara ne kan tuntuba, tattaunawa da kuma yin la’akari da dukkan batutuwa da kuma bukatu da muradu daban-daban a fadin kasar nan, tare da manufar tabbatar da ganin an karfafa hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Don haka jam’iyyar PDP ta bukaci ‘yan Najeriya, da mambobi da magoya bayansu da su yi watsi da ikirarin da ba ta da tushe balle makama, jam’iyyar ta kuma gargadi masu da’awar cewa su daina kai tsaye.
