Jam’iyyar Labour Ta Bukaci Cikakken Iko Ga Kananan Hukumomi

Labour Party
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Bayan zama da majalisar wakilai na kasa tayi game da dokar zabe, jam’iyyar Labour ta bukaci a bada cikakken iko ga kananan hukumomi tare da bukatar a sauke dokar hukumar zabe na jihohi SIEC inda tace duk gyarar doka da za’a yi wanda bazai ba kananan hukumomin yancin gashin kai ba da kuma sauke dokar na SIEC, to anyi shine kadai ga masu fada aji na siyasa.

Jam’iyyar ta bukaci gyarar dokar taba hukumar zabe mai zaman kanta na INEC nauyin gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar.

Hakan yana kunshe cikin sanarwa da sakataren majalisar Mr. Julius Abure ya fitar

Mr Abure ya bukaci yan majalisar dasu daura dammarar su suyi amfani da damar gyare-gyaren daidai da bukatu da muradun al’umma.

Haka zalika jam’iyyar Labour ta kuma bukaci majalisar da tayi gyarar doka da zai bada damar amfani da na’urar fasaha a zabe da nufin saukakewa jama’a masu bukatu na musamman da masu nakasa da ma kuma bunkasa kasantuwar matasa cikin zabe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply