Jamhuriyar Benin Bata Da Ra’ayin Kasancewa Wani Bangare A Najeriya.

250px-map_of_aouzou_stip_chad-svg-svg
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An ja hankalin ministan harkokin kasashen waje kan rahoton da ya zaga kafafen sadarwa na cewa jamhuriyar Benin zata zama jiha na 37 a kasar Najeriya.

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama yayin da suke tare da takwarar sa na jamhuriyar Benin ya tattaunawa da manema labarai bayan taron da suka gudanar tsakanin tawagar ministoci daga kasashen biyu.

Shugaban kasar Benin yace yana so alakar kasashen biyu ya kara dorewa kamar dai jamhuriyar ya kasance jiha na 37 a kasar Najeriya.

Kasar Najeriya dai bata da wani bukatar maida jamhuriyar Benin wani bangare a Najeriya.

Daga karshe ministan yayi kira ga jama’a da cewa suyi watsi da irin wannan labari mara tushe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply