IPMAN Ta Umarci Mambobinsu Dasu Saida Man Fetur Kan Naira 162

ipman
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar masu saida man fetur ta najeriya wato IPMAN reshen jihar Kano ya bukaci mambobinta dasu shirya saida man akan Naira 162.44 kan kowace litar man kamar yadda gwamnatin tarayya ta bada umarni.

Shugaban kungiyar ta IPMAN na Kano Alhaji Bashir Dan-Malam ne ya bada umarnin ranar litinin a taron da suka gudanar a jihar Kano.

Dandal Kura Radio International ta gano cewa gwamnatin tarrayya ta rage kudin man fetur din daga naira 168 zuwa Naira 162.44 kan kowace lita bayan tattaunawar su da kungiyar kwadago.

Haka nan yace umarnin ya biyo bayan rage farashin kayan da hukumar man fetur ta kasa tayiwa kungiyar daga naira 153.17 zuwa 148.17 kan kowace lita daga ranar Litinin.

Acewarsa tunda gwamnatin tarayya tabrage kudin da Naira 5 don haka suma dole su rage farashin man a gidajen man ga mutane.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply